Minna: IBB ya yaba wa gwamna Wike game da kokarin sake farfado da PDP

Minna: IBB ya yaba wa gwamna Wike game da kokarin sake farfado da PDP

- IBB ya yaba wa gwamnan jihar Ribas game da kokarin sake farfado da jam’iyyar PDP

- Wike ya jagoranci wasu shugabannin jihar Ribas zuwa ziyarar tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Hilltop a Minna

- IBB ya ce yana alfahari da gwamnan game da kyakyawar shugabancin sa

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya yaba wa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, game da kokarin da yake yi wajen inganta harkokin siyasa a Najeriya.

Da yake jawabi a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba a lokacin da gwamnan Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya jagoranci wasu shugabannin jihar Ribas zuwa ziyarar sa a gidansa da ke Hilltop a Minna, babban birnin jihar Neja, tsohon shugaban kasar, ya yaba wa gwamna game da kokarin farfado da jam'iyyar PDP.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, IBB ya lura cewa kasar tana buƙatar wata jam’iyyar adawa mai karfi.

Minna: IBB ya yaba wa gwamna Wike game da kokarin sake gina PDP

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike

Ya ce: "Shi ya sa nake yaba kokarin da gwamnan jihar Ribas ke yi don tabbatar da cewa ana yin siyasa ta hanyar da ta dace a kasar kamar yadda ake yi a kasashen duniya da suka ci gaba”.

KU KARANTA: Abinda Shugaba Buhari ya zayyana wa shugaban Kasar Togo a ganawar su

IBB ya gode wa gwamnan game da kyakyawar shugabancin sa. Ya ce labarin nasarorin gwamna Wike sananne ce.

Da yake jawabi game da zaben Anambra, tsohon shugaban sojan Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce, an yi zaben da gaskiya. Ya ce bai yi mamakin sakamakon zaben ba, saboda an shirya wa zaben.

Ya ce: "Wannan ya nuna cewa 'yan Najeriya zasu iya gudanar da kansu a cikin zaman lafiya".

Da yake jawabi ga 'yan jarida bayan ziyarar, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce shugabannin jihar sun kasance a Minna don neman shawarar shugaban a matsayin shugabannin PDP.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel