Nigerian news All categories All tags
Shugaban rundunar tsaro ya kai ziyarar aiki yankin Arewa maso Gabas

Shugaban rundunar tsaro ya kai ziyarar aiki yankin Arewa maso Gabas

- Shugaban rundunar tsaro, Janar Abayomi Olanisakin ya kai ziyarar aiki yankin Arewa maso Gabas

- Olanisakin ya kai ziyarar ne domin ya gane ma idanun shi halin da sojojin ke ciki kuma ya samu bayannai kan nasarorin da suke samu da akasin haka

A yau Laraba ne shugaban rundunar tsaro, Janar Abayomi Olonisakin, ya fara aikin ziyarar dakarun sojin da ke yaki da yan ta'adar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban rundunar tsaro ya kai ziyarar aiki yankin Arewa maso Gabas

Shugaban rundunar tsaro, Abayomi Olonisakin.

Shugaban ya ziyarci sansanin soji na bada umarni da kuma sasanin sojin da ke karkashin Operation Lafiya Dole duk dai a garin Maidugurin.

Kwamandan rundunar Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, yace ziayarar na daya daga cikin ayyukan shugaban rundunar tsaron.

DUBA WANNAN: Bamu amince da aurar da kananan yara ba - Inji Kungiyar NASFAT

Attahiru ya bayyana cewa zai gabatar ma shugaban rundunar tsaron duk bayanan ayyukan da rundunar take gudanar wa da kuma bayanai akan yakin da sukeyi da yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa masa Gabas din.

Hukumar dillancin labaran Najeriya, NAN ta ruwaito cewa Olonisakin yana tare da manyan hafsoshin soji da yan sanda a yayin da ya kai ziyarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel