Nigerian news All categories All tags
Mutane 7 sun rasa rayukan su ta sanadiyar hatsarin motar a Kano

Mutane 7 sun rasa rayukan su ta sanadiyar hatsarin motar a Kano

- Motar tawagar kungiyar ma'aikatan kiwon lafiya ta yi hatsari akan hanyar Kano zuwa Kaduna

- Ma'aikatan sun yi hatasarin ne a lokacin da suke kan hanyar zuwa taron kungiya ma'aikatan kiwon lafiya a Keffi

Mutane bakwai daga cikin kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya sun rasa rayukan sa ta sanadiyar hatsarin mota da ya auku akan hanyar Kano zuwa Kaduna a kauyen Rikolo a ranar Talata 21 ga watan Nawumba.

Ma'aikatan sun mutu ne a lokacin da suke kan hanyar zuwa taron kungiya ma'aikatan kiwon lafiya a Keffi, jihar Nasarawa

Mutane 7 sun rasa rayukan su ta sanadiyar hatsarin motar a Kano

Mutane 7 sun rasa rayukan su ta sanadiyar hatsarin motar a Kano

Rahotanni sun nuna cewa motar ta kubce ma direban ne a lokacin da yake kokarin kauce ma wani babban rami da misalin karfe 3.00pm na ranar Talata.

KU KARANTA : Siyasa: Ana rade-radin Buhari zai yiwa sanata Kwankwaso tayin minista

Shugaban Asibitin koyarwa na Aminu Kano, Kwamred Sarki Adamu ya tabbatar da aukuwan wannan lamari.

Yace mutane 6 sun muta a take wajen, sai kuma na 7 ya cika a asibitin Shika dake Zaria.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel