Nigerian news All categories All tags
Abun da Alex Ekueweme yayi wa Dimokradiyyar Najeriya – Jerry Gana

Abun da Alex Ekueweme yayi wa Dimokradiyyar Najeriya – Jerry Gana

- Ferfesa Jerry Gana yayi wa iyalan Alex Ekueweme ta'aziyar mutuwar sa

- Tsoho ministar ya ce yan Najeriya ba za su taba mantawa da irin gudnumawar da Ekueweme ya ba dimokradiyyar Najeriya ba

- Marigayi Alex Ekueweme yana daga cikin jigajigan da suka kafa jam'iyyar PDP a Najeriya

Tsohon ministar watsa labaru Ferfesa Jerry Gana, ya ce Alex Ekueweme ya rayu ne akan yiwa Najeriya bauta.

Alex Ekwueme yana daga cikin yan Najeriya da suka tabbatar da mulkin dimokradiyya ta kafu Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yana daga cikin jigajigan da suka kafa jam’iyyar People’s Democratic Party PDP a Najeriya.

Abun da Alex Ekueweme yayi wa Dimokradiyyar Najeriya – Jerry Gana

Abun da Alex Ekueweme yayi wa Dimokradiyyar Najeriya – Jerry Gana

KU KARANTA : Atiku ya bayyana hanyoyin da za a iya kawo karshen hare-haren kunar bakin wake a Najeriya

Kuma yan Najeriya ba za su taba mantawa da gudumawar da wannan bawan Allah yaba wa dimokradiyyar Najeriya ba.

Jerry Gana yayi wannan jawabin ne a lokacin da yake mika ta’aziyar sa ga iyalan Alex Ekueweme.

Dakta Alex Ekwueme tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya na biyu tsakanin shekara 1979 da 1983 ya rasu a ranar Lahadi 20 ga watan Nawumba shekara 2017 a Asibitin Landan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel