Majalisar Dokokin Zimbabwe zata fara yunkurin tsige Shugaba Robert Mugabe

Majalisar Dokokin Zimbabwe zata fara yunkurin tsige Shugaba Robert Mugabe

Rahotanni sun kawo cewa a yau Talata, 21 ga watan Nuwamba ne ake sa ran Majalisar kasar Zimbabwe zata fara yunkurin tsige shugaban kasar ta Robert Mugabe, sai dai yunkurin na iya ‘daukar lokaci mai tsawo da sarkakiya ko kuma ya zamanto bai yi tasiri ba.

Kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe ya shimfida wasu shuruda hudu da za a iya tsige shugaban kasa akan su.

Wadanda suka hada da tafka kuskure mai girma da rashin biyayya da rashin aiki da kundin tsarin mulkin kasa da kuma gaza yin aiki a matsayin shugaban kasa saboda matsalar nakasa ko gushewar hankali.

Majalisar Dokokin Zimbabwe zata fara yunkurin tsige Shugaba Robert Mugabe

Majalisar Dokokin Zimbabwe zata fara yunkurin tsige Shugaba Robert Mugabe

Kamar yadda kuka sani lokacin da sojoji suka yi masa daurin talala sun bashi damar kare mutuncinsa amma Mugabe ya yi biris.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana! EFCC ta samu hurumin tsare tsohon Sakataren gwamnati kwana 30

Shugaba Mugabe yayi kunnen uwar shegu da wa'adin da jam'iyyarsa ta deba masa na ya bar mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel