Rikita-Rikita: Sabon rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU game da kwangen Naira biliyan 5

Rikita-Rikita: Sabon rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU game da kwangen Naira biliyan 5

Sabon rikici na shirin sake kunno kai a tsakanin gwamnatin shugaba Buhari ta tarayya da kuma kungiyar malaman jami'oi na ASUU saboda zargin kwange wajen basu kudun su da suka kai akalla Naira biliyan 5.

Wannan alamu dai na kunnowar rikicin mun same shi ne jim kadan bayan kammala wani babban muhimmin taro na masu ruwa da tsaki na majalisar zartarwar kungiyar a satin da ya gabata a Abuja babban birnin tarayya.

Rikita-Rikita: Sabon rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU game da kwangen Naira biliyan 5

Rikita-Rikita: Sabon rikici tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU game da kwangen Naira biliyan 5

KU KARANTA: Yadda na hana zurarewar kudade daga ma'aikata ta - Pantami

Legit.ng dai ta samu cewa kungiyar ta ASUU tuni har ta kafa wani kwakkwaran kwamiti da zai shawarce ta game da yadda zata bullowa lamarin a dukkan rashinan kungiyar dake a jami'oin tarayyar kasar nan.

Tun farko dai abun da ake kyautata zaton ya jawo wannan badakalar shine zargin da gwamnatin tarayya ke yi ma kungiyar ta ASUU na rashin biyan kudin haraji a kasa, zargin da su kuma kungiyar suka karyata da cewa su ba kasuwanci suke yi ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel