Ba zan taba zama karen farautar Ganduje ba - Kakakin majalisar Kano

Ba zan taba zama karen farautar Ganduje ba - Kakakin majalisar Kano

Kakakin majalisar jihar Kano Honorable Yusuf Ata ya sha alwashin cigaba da zama mai anfani da kuma ra'ayin kansa yayin da yake jagorantar 'yan majalisar jihar wajen ganin ba su zama 'yan amshin shata ba ga gwamna da kuma gwamnatin jihar kamar dai yadda dokar kasa ta tanadar.

A cewar sa: "Tarihi na a siyasance a matsayin dan majalisa ba 'a tana samu na da zama dan amshin shata ba ko kuma karin farautar wani a don haka kuma yanzu ba zai fara ba."

Ba zan taba zama karen farautar Ganduje ba - Kakakin majalisar Kano

Ba zan taba zama karen farautar Ganduje ba - Kakakin majalisar Kano

KU KARANTA: Za'a dawo da jiragen saman Najeriya - Buhari

Legit.ng ta samu cewa kakakin majalisar ya bayyana hakan ne a kwanan baya inda ya kara jajjada aniyar sa ta ci gaba da jagorantar dukkan sauran 'yan majalisun 40 a bisa adalci da kyakkyawan shugabanci.

Haka nan kuma Alhaji Ata ya kara da cewa majalisar zata yi karatun ta natsu da kuma binciken kwakwaf ga dukkan abubuwan da ke kunshe a cikin kasafin kudin jihar domin samun kyakkyawan wakilci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel