Makarfi ya kawo wa jam'iyyar PDP bakin jini inji Sanata a jam'iyyar

Makarfi ya kawo wa jam'iyyar PDP bakin jini inji Sanata a jam'iyyar

Sanatan dake wakiltar mazabar jihar Ogun ta gabas a majalisar dattijai mai suna Buruji Kashamu ya bayyana zuwan Sanata Ahmad Makarfi da zaman sa shugaban jam'iyyar PDP a matsayin wani mugun abu da ba abun da ya kawo wa jam'iyyar sai bakin jini da rashin sa'a.

Sanatan dai yayi wannan ikirarin ne da yake tofa albarkacin bakin sa game da sakamakon zaben da ya gudana a jihar Anambra karshen sati da kuma yadda jam'iyyar ta PDP ta kasa tabuka komai a zaben.

Makarfi ya kawo wa jam'iyyar PDP bakin jini inji Sanata a jam'iyyar

Makarfi ya kawo wa jam'iyyar PDP bakin jini inji Sanata a jam'iyyar

KUKARANTA: Jiga-jigan jam'iyyar PDP 19 sun koma APC a Katsina

Legit.ng dai ta samu cewa Sanatan ya bayyana irin buguwar rawar da jam'iyyar ta taka a inda ta zo a matsayi na 3 a matsayin abun kunya da kuma bisa dalilin bakin jinin da shugaba Makarfi ya kawo masu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa hukumar zabe ta kasa tuni ta sanar da cewar Gwamna mai ci shine ya lashe zaben da gagarumin rinjaye yayin da jam'iyyar APC mai mulki ya tarayya ta zo na biyu sai kuma PDP da ta zo na 3.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel