Kisan Bilyamin: Yan sanda sun samu faifan bidiyon abun da ya faru, sun kama masu gadin gidan

Kisan Bilyamin: Yan sanda sun samu faifan bidiyon abun da ya faru, sun kama masu gadin gidan

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya sun bayyana cewa sun samu faifan bidiyon ainihin abun da faru da har yayi sanadiyyar ajalin dan tsohon shugaban PDP Bilyaminu Bello da ake zargin matar sa Maryam Sanda da yi a gidan su.

Tun farko dai majiyar mu ta samu cewa matar ta sa ta caka masa wuka ne dai sau da yawa a cikin sa da kuma al'aurar sa bayan da ta zarge sa da shirin kara aure kafin daga bisani ya rasu.

Kisan Bilyamin: Yan sanda sun samu faifan bidiyon abun da ya faru, sun kama masu gadin gidan

Kisan Bilyamin: Yan sanda sun samu faifan bidiyon abun da ya faru, sun kama masu gadin gidan

KU KARANTA: Dangote ya bayar da sadaka ta makudan kudade

Legit.ng dai ta samu cewa wani babba a rundunar 'yan sandan dai ya bayyana cewa sun samu faifan ne ta hanyar na'urar daukar hotunan sirrin nan ta CCTV kuma yanzu haka ma dai sun kama sauran masu gadin gidan da na'urar ta nuna suna taimakawa matar wajen daukar mijin zuwa cikin mota.

A jiya ma dai mun samu cewa jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja sun bayyana cewa tuni har sun fara kaddamar da wani muhimmin bincike a game da kisan Bilyamin, dan tsohon Ciyaman na kasa a jam'iyyar PDP, Muhammad Bello.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel