Badakalar Naira biliyan 2.1: Maina ya kalubalanci EFCC zuwa muhawara a bainar jama'a

Badakalar Naira biliyan 2.1: Maina ya kalubalanci EFCC zuwa muhawara a bainar jama'a

Tsohon shugaban kwamitin lalubo hanyar gyara na harkokin fanshon kasa da tsohon shugaban kasa ya kafa a shekarun baya watau Presidential Pension Reform Team, PPRT da a yanzu haka yake a wata maboya ya kalubalanci hukumar EFCC ya zuwa muhawara a bainar jama'a game da kudin da ake zargin ya sata.

A cewar sa: "Bari in fada da babbar murya cewar ina gayyatar hukumar EFCC zuwa muhawara a bainar jama'a karkashin jagorancin wasu mutane adilai idan har da gaske. Suna da gaskiya a game da zarge-zargen da suke yi mani".

Badakalar Naira biliyan 2.1: Maina ya kalubalanci EFCC zuwa muhawara a bainar jama'a

Badakalar Naira biliyan 2.1: Maina ya kalubalanci EFCC zuwa muhawara a bainar jama'a

KU KARANTA: Wasu malamai sun kara faduwa jarabawa

Legit.ng dai ta samu Abdurrasheed Maina yayi wannan kalamin ne a ta bakin Lauyan sa Sani Katu a garin Kaduna yayin da kuma ya kara jaddada cewar shi fa bai da laifi ko kadan.

Haka nan kuma sai sanarwar ta cigaba da zayyano irin makudan kudaden da ko dai Maina din ya kwato daga hannu wasu barayi ko kuma ya toshe hanyar satar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel