Karin daraja: Buhari ya kai Najeriya matsayi na 35 a jadawalin kyakkyawan shugabanci

Karin daraja: Buhari ya kai Najeriya matsayi na 35 a jadawalin kyakkyawan shugabanci

Wani sabon rahoto da ya fita ya nuna cewa kasar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta kai a matsayi na 36 daga cikin 54 na kasashen nahiyar Afrika a bisa ma'aunin kyakkyawan shugabanci kamar da yadda wata gidauniyar Month Ibrahim ta fitar.

Duk da dai cewa Najeriya din ta kara samun matsayi sosai a bisa sikalen kyakkyawan shugabancin musamman ma a cikin shekaru 5 da suka gabata, amma sai dai kasar ta samu maki 48.1 ne a cikin 100 da kuma hakan ya sanya ta zama a kasan kasar Afrika ta kudu da ta samu 50.8.

Karin daraja: Buhari ya kai Najeriya matsayi na 35 a jadawalin kyakkyawan shugabanci

Karin daraja: Buhari ya kai Najeriya matsayi na 35 a jadawalin kyakkyawan shugabanci

KU KARANTA: Yadda abokai da 'yan uwa sukayi burus da tsohon shugaba Jonathan

Legit.ng dai ta samu cewa kasar ta Najeriya ta samu makin da ya fi yawa ne a wajen samar da kyakkyawan shugabancin da ke bayar da damar sa hannun 'yan kasa da kuma 'yancin yan adam inda ta samu maki 52.5.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a satin da ya gabata ma dai shugaba Buhari ya bayyana cewa yanayin salon mulkin sa na cigaba da karawa kasar daraja da kima a idon duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel