Siyasa: Fayose ya musanta jita-Jitar sauya sheka zuwa APC

Siyasa: Fayose ya musanta jita-Jitar sauya sheka zuwa APC

- Gwamnan jihar Ekiti ya ce ya nan daram a PDP bayan zargin ficewa daga jam’iyyar

- Fayose ya ce jita-jitar aikin hannun jam'iyyar APC ne wanda ta ke kuma ɗaukan nauyin yaɗawa

- Gwamnan ya ce sauya sheka zuwa APC tamkar bijirewa Yesu Kiristi ne

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya karyata zargin cewa yana shirin sauya sheka daga babbabn jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar da ke mulki ta APC, ya ce waɗannan jita-jitar ba gaskiya ba ne.

Sakataren hulɗa da jama'a ga gwamna Fayose, Mr. Idowu Adelusi, ya bayyana hakan a wata sanarwar gwamnan da ya fitar. A cikin sanarwar Fayose, ya ce, wannan jita-jitar aikin hannun jam'iyyar APC ne wanda ta ke kuma ɗaukan nauyin yaɗawa.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fayose ya bayyana a sanarwar cewa a wajensa sauya sheka zuwa APC tamkar bijirewa Yesu Kiristi ne.

Siyasa: Fayose ya musanta jita-Jitar sauya sheka zuwa APC

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose

"A lokacin da PDP ke tsaka mai wuya da rikicin shugabanci ta dabaibaye ta, Fayose bai yi tunanin ficewa daga PDP ba, sai yanzun da komai ya warware, jam'iyyar na shirin karɓe ragamar mulki a zaɓe mai zuwa na shekarar 2019, wai shi ne za a yaɗa cewar, ina shirin barin jam’iyyar", a cewar sanarwar.

KU KARANTA: An yabawa Shugaba Buhari game da gudanar da zaben Anambra

Sanarwar ta ci gaba da cewa, "Babban kalubale da ke gaban gwamnan a halin yanzu shi ne, shirya hada-hadar yadda zai miƙa ragamar mulkin jihar Ekiti ga wani ɗan PDP a shekara ta 2018".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel