Nigerian news All categories All tags
Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

- Shugaba Buhari zai kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen sama

- An warewa jiragen sama da Naira Biliyan 7 a kasafin shekarar 2018

- Ana kashe makudan kudi wajen kula da jiragen Shugaban Kasar

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta kashe makudan kudi wajen sha’anin jirgin saman da yake amfani da su a wannan shekarar.

Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Wasu daga cikin jiragen saman Shugaban Kasa

A kasafin kudin bana kamar yadda Jaridar Premium Times ta gano za a kashe sama da Biliyan 7 wajen mai da gyaran jirgin Shugaban kasa da kuma jigila da sayen mai. Za a kashe kusan Biliyan 3 ne wajen sayen wasu kaya na jiragen.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dage wajen sha’anin jirgin sama

Kasafin kudin bana dai ya ma nuna cewa kudin da za a kashe kan jiragen Shugaban Kasar ya karu ne daga abin da aka ware a bara. A 2017 an warewa jiragen Naira biliyan 4 ne rak amma yanzu an samu karin kusan kashi 70% a 2018.

Akwai jirage 5 na Shugaban Kasa wanda kula da su ya zama aiki a Kasar don haka ne ma Shugaban Kasa Buhari ya rabu da wasu daga ciki bayan hawan sa mulki. Za a kashe kudi har wajen sa wa jiragen Talabijin kai tsaye da kuma yanar gizo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel