Nigerian news All categories All tags
Yau ake shirin tsige Shugaba Robert Mugabe daga mulki

Yau ake shirin tsige Shugaba Robert Mugabe daga mulki

- Yau ake tunani za a iya sauke Shugaba Mugabe daga mulki

- Jam’iyyar ZANU-PF mai mulki za ta tsige Shugaban na ta

- Shugaba Robert Mugabe ya ki yin murabus a shekaran jiya

Dama kun ji cewa ana shirin sauke Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ba girma ba arziki bayan da ya ki sauka daga mulkin cikin ruwan sanyi. Da zarar an samu kaso 2 cikin 3 na ‘Yan Majalisa za a tsige Shugaban.

Saura kiris: 'Yan Majalisa na daf da tsige Shugaba Mugabe

Ana yunkurin tsige Shugaban Kasa Mugabe

Mun samu labari daga gidan yada labarai na Duniya na AFP cewa wani babban Jami’in Gwamnatin Kasar ya bayyana cewa yau Talata Jam’iyyar ZANU-PF za ta fara kokarin tsige Shugaban na ta Robert Mugabe daga mulki.

KU KARANTA: Ana yunkurin sauke Shugaba Mugabe daga mulki

A yau dinnan ne ake sa rai Majalisa ta fara tattauna game da yunkurin tsige Shugaban Kasar. Za a nada kwamitin ‘Yan Majalisa da za su duba batun a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai na Kasar kamar yadda mu ka ji.

Paul Mangwana wani ‘Dan Majalisa daga cikin ‘Yan Majalisar ZANU_PF mai rinjaye ya tabbatar da cewa an yi an gama. Dama dai ‘Yan Jam’iyyar adawa ba su tare da Mugabe ga kuma Jam’iyyar sa ta ZANU sun bi sahun tsige sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel