Nigerian news All categories All tags
Malamai 51 sun fadi jarrabawar malanta a Legas – TRCN

Malamai 51 sun fadi jarrabawar malanta a Legas – TRCN

- Wasu Malaman Legas sun fadi jarrabawar TRCN ta koyarwa

- Sama da Malamai 400 su ka rubuta jarrabawar kwanan nan

- Sai dai da kamar wuya a kori Malaman Jihar a wannan mataki

Mun samu labari cewa wasu Malaman Makaranta a Jihar Legas sun fadi jarrabawar koyarwa da Hukumar rajistar Malamai ta kasa ta gudanar. Daga ciki har da wani mai PhD da kuma masu Digiri na 2 har 282 sannan masu Digiri da NCE.

Malamai 51 sun fadi jarrabawar malanta a Legas – TRCN

Wasu Malaman da su ka fadi jarrabawa a Kaduna

Malamai 51 ne su ka gaza cin jarrabawar da Hukumar nan ta TRCN mai rajistar Malaman Najeriya ta gudanar da ake kira PQE. A cikin Malamai sama da 400 da su ka zauna jarrabawar an samu wasu 51 da ba su samu nasara ba.

KU KARANTA: Sallamar Malamai: Babban Malamin addini ya ba El-Rufai shawara

Gbolohan Enilobo wanda shi ne Shugaban Hukumar na Yankin Legas ya bayyanawa manema labarai wannan a jiya Litinin. Enilobo yace Malaman da su ka fadi sun samu matsalar amfani ne da na’ura mai kwakwalwa ta zamani.

Idan ba a manta ba a tsakiyar watan jiya na Oktoba ne aka yi wa Malaman wannan jarrabawa. Za a ba wadanda su ka fadi dama har sau 3 domin su kara jarraba sa’a wanda idan abin ya gagara bayan nan za a sallame su watau ba su ba malanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel