Nigerian news All categories All tags
Yan sanda sun soma bincike na musamman game da kisan Bilyamin, dan tsohon ciyaman din PDP

Yan sanda sun soma bincike na musamman game da kisan Bilyamin, dan tsohon ciyaman din PDP

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar garin Abuja sun bayyana cewa tuni har sun fara kaddamar da wani muhimmin bincike a game da kisan Bilyamin, dan tsohon Ciyaman na kasa a jam'iyyar PDP, Muhammad Bello.

Jami'ain hulda da jama'a na rundunar DSP Anjuguri Manzah shine ya sanar da hakan a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a yau Litinin a can garin na Abuja.

Yan sanda sun soma bincike na musamman game da kisan Bilyamin, dan tsohon ciyaman din PDP

Yan sanda sun soma bincike na musamman game da kisan Bilyamin, dan tsohon ciyaman din PDP

KU KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban kasa Alex Ekwueme ya mutu

Legit.ng ta samu dai cewa DSP Manzah ya kara da cewa tun da suka samu labarin faruwar lamarin, sai suka kafa wata muhimmiyar runduna da zata fara bincike na musamman tun daga inda lamarin ya faru don gano musabbabin lamarin.

Ya kara da cewa bayan bincike na farko-farko dai, tuni yan sandan suka cafke matar da ake zargi da aikata kisan inda yanzu haka take a tsare sannan kuma ya tabbatar da cewa doka zata hau kanta.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel