Duk da kokarin Super Eagles Najeriya tayi kasa a teburin FIFA

Duk da kokarin Super Eagles Najeriya tayi kasa a teburin FIFA

- Kwanan nan Najeriya ta ba Kasar Argentina kashi

- Sai dai Najeriya za ma ta kara yin kasa ne inji FIFA

- Super Eagles ta sauka a Afrika kamar yadda za aji

Abin da ba ban mamaki don kuwa duk da irin kokarin da Kungiyar Super Eagles ta Najeriya tayi, ta kuma sha kasa a teburin FIFA na Duniya.

Duk da kokarin Super Eagles Najeriya tayi kasa a teburin FIFA

Super Eagles ta ba Kasar Argentina kashi

A wasan kwanan nan ne Najeriya ta lallasa Kasar Argentina da ci 4-2 amma duk da haka labari yana zuwa mana cewa Kasar ta ma kara yin kasa ne a matakin da Hukumar kwallo na Duniya watau FIFA za ta fitar a Ranar Alhamis.

KU KARANTA: Ana kokarin sauke Mugabe daga kujera

A cewar Daily Trust Kungiyar Super Eagles ta Najeriya da ke na 5 a Afrika za ta zazzago da kusan mataki 3. Yanzu a Nahiyar Afrika Kasar Morocca ce ta dawo ta 5. Sanagal ce ta farko a Afrika yayin da ta buge Tunisiya da Kasar Misra bayan ta ci wasan ta.

Kasar Kongo ma dai yanzu ta sha gaban Najeriya ganin cewa wasan da Najeriya ta buga a wancan makon na motsa jini ne kurum. Yanzu dai Najeriya na da maki 671 wanda ke nuna cewa an sha gaban ta a teburin matakin kasashen Duniya na FIFA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel