Allah Sarki: Maras lafiya ya samu gudumawar Naira Miliyan 10

Allah Sarki: Maras lafiya ya samu gudumawar Naira Miliyan 10

- Sadiq Daba da ke fama da rashin lafiya ya samu gudumuwa

- Wani Bawan Allah daga can Amurka ya kawowa Daba dauki

- Mr. Soni Irabor ne ke cigaba da hada kudin asibitin mai jinyar

Za ku ji mun samu labarin cewa fitaccen ‘Dan wasan nan na kasar nan Sadiq Daba da ke kwance yana jinya ya samu gudumawar Naira Miliyan 10.

Allah Sarki: Maras lafiya ya samu gudumawar Naira Miliyan 10

An ba Daba gudumawar Naira Miliyan 10

Wani Bawan Allah mai suna Max Collins ya bayyana wannan a shafin sa na Facebook a jiya inda yace wani mutumi mai suna Cif Kenny Martins ne yayi wannan kokari. Sadiq Daba da ya dade yana jinya ya samu kyautar gagrumar gudumuwa.

KU KARANTA: Za a samawa mutane da dama aiki a Najeriya - NNPC

Yanzu haka dai an samu makudan miliyoyin da ake bukata na yi wa wannan maras lafiya magani. Wannan Bawan Allah ya taimaka ne bayan da aka kira shi daga Kasar Amurka nan take yayi alkawarin agazawa wannan mutumi.

Abubakar Sadiq Daba dai bai taba kai kukan sa a fili ba amma jama’a na ta taimaka sa da kudi ta asusun bankin sa. Yanzu haka dai kokon-baran na bude inda jama’a ke cigaba da bada gudumuwar su domin ganin ya samu sauki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel