Yola: Manoma 10,000 zasu amfana da shirin bunkasa aikin noma a Adamawa

Yola: Manoma 10,000 zasu amfana da shirin bunkasa aikin noma a Adamawa

- Manoma 10,000 zasu amfana da shirin bunkasa aikin noma a jihar Adamawa

- Kwamishinan aikin gona ya ce kowane manoma suna da damar samun tsakanin kadada 1 zuwa 3

- Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta hada hannu tare da sarakunan gargajiya a duk inda ake buƙatar filin noma

Kwamishinan aikin gona na jihar Adamawa, Ahmadu Waziri, ya ce an kammala shirin shigar da manoma 10,000 a jihar a cikin shirin bunkasa aikin noma na hadin gwiwar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar ci gaban aikin gona (AADS).

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Waziri ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba a wani taron tattaunawa wanda aka shirya wa wakilan manoman jihar a kan wannan shirin.

A cewarsa, shirin, wanda ke da mahimmanci a karkashin shirin Anchor Borrowers’ Programme wanda aka yi domin matasa marasa aikin yi wadanda suke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 kuma a halin yanzu ba su cin moriyar irin wannan shirin na gwamnati.

Yola: Manoma 10,000 zasu amfana da shirin bunkasa aikin noma a Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Jibrilla Bindow

Ya ce Adamawa ta shiga bangaren masara da kiwon dabbobi kamar yadda ta zaɓa a karkashin shirin, ya kara da cewa kowane matashi zai iya amfana daga wannan shirin.

KU KARANTA: Shekarau ya yaba ma gwamna Ganduje bisa inganta harkar lafiya a jihar Kano

Waziri ya bayyana cewa a karkashin shirin, gwamnatin jihar za ta samar da filin noma kyauta ga wanda suka amfana, inda ya kamata, yayin da kowane manoma suna da damar samun tsakanin kadada 1 zuwa 3.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta hada hannu tare da sarakunan gargajiya a duk inda ake buƙatar fili.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel