Najeriya za ta maida hankali wajen gyara harkar jirgin sama – Shugaba Buhari

Najeriya za ta maida hankali wajen gyara harkar jirgin sama – Shugaba Buhari

- Gwamnatin Buhari za ta maida hankali wajen harkar jirgin sama

- Minista Hadi Sirika da Shugaban ICAO sun gana Shugaba Buhari

- An ga matukar canji a fannin jirgin sama a Najeriya kwanan nan

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta dage wajen kafa jiragen saman Najeriya inji ta bakin mai magana da yawun Shugaban Kasar Garba Shehu. Shugaban ya koka da yadda jirgin saman Najeriya ya mutu a baya.

Shugaban Kasa Buhari ya bayyana cewa Najeriya za ta maida hankali wajen gyara harkar jirgin sama a Gwamnatin sa. Shugaban Kasar yayi wannan jawabi ne bayan ya gana da Shugaban Kungiyar ICAO na Duniya Aliu Muyiwa a Fadar Shugaban Kasa.

KU KARANTA: Ba zu mu goyi bayan Gwamnatin Buhari ba - Ango Abdullahi

Shugaba Buhari ya karbi kyaututtukan da Najeriya ta samu a harkar jirgin sama kwanan nan saboda kokarin Gwamnatin Kasar. Sannan Shugaba Buhari ya nuna goyon bayan sa na kafa jirgin sama na Kasar inda yace Najeriya ya dace ace tana da jiragen kan ta.

Ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika ya bayyanawa Shugaban Kasar cewa wannan karo za ayi babban taron da ya shafi harkar jirgin sama a Najeriya inda duk wasu manya a harkar za su hallara kasar. A baya dai an saba yin wannan taro ne a Kanada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel