Shugaba Mugabe ya hakura da mulkin Zimbabwe

Shugaba Mugabe ya hakura da mulkin Zimbabwe

- Ana shirin sauke Shugaba Mugabe ba girma ba arziki

- Tun kwanaki Sojojin Kasar su ka tsare Robert Mugabe

- R. Mugabe yayi shekaru fiye da 30 yana mulki a Kasar

Yanzu haka Shugaban kasa Robert Mugabe na Kasar Zimbabwe zai sha kunya don kuwa ana yunkurin sauke sa daga mulki da karfi da yaji.

Shugaba Mugabe ya hakura da mulkin Zimbabwe

Ana yunkurin sauke Shugaba Mugabe

Shugaba Robert Mugabe ya ba Duniya mamaki a jiya bayan da aka gama shiryawa da shi cewa zai bayyanawa Jama’a cewa yayi murabus sai ga shi ya gagara yin haka. Amma yanzu mu na samun labari cewa Shugaban ya hakura zai sauka.

KU KARANTA: Sojoji sun ja kunnen Shugaba Mugabe a Kasar Zimbabwe

Robert Mugabe ya shirya sauka daga mulki kamar yadda Gidan CNN ta rahoto. Yanzu haka Mugabe zai nemi a kyale sa da iyalin sa su tsere daga kasar cikin ruwan sanyi. Idan dai Shugaban bai sauka ba, Majalisar Kasar za ta tsige sa.

Tuni dai aka fara zanga-zanga a babban Birnin Kasar na Harare inda ake nema Robert Mugabe ya fice. Shugaba Mugabe ya dade yana mulki a Kasar ta Afrika ana kuma ganin cewa yana da niyyar daura matar sa Grace Mugabe kan mulkin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel