Zaben Anambra: Dan takara na PDP, Obaze ya yi amai ya lashe

Zaben Anambra: Dan takara na PDP, Obaze ya yi amai ya lashe

- Mista Oseloka Obaze, dan takara na PDP ya janye rashin amincewarsa ga sakamakon zaben Anambra

- Obaze ya ce yanzu ya yi tawakali, ya taya gwamnan da mataimakinsa murna

- A farko Obaze ya ki amince da sakamakon zaben, ya ce an tafka babban magudi

Mista Oseloka Obaze, dan takara na babban jam'iyyar adawa ta PDP a zaben Anambra, ya sake lale yayin da ya amince da nasarar gwamna Willie Obiano a zaben jihar Anamba.

Obaze ya ki amincewa da sakamakon zaben bayan da hukumar INEC ta sanar, yana zargin rashin daidaito a sakamakon.

Obaze a wani taron manema labarai a Awka a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, ya mika sakon taya Obiano murna, ya ce ya yi tawakali da abin da ya faru.

Zaben Anambra: Dan takara na PDP, Obaze ya yi amai ya lashe

Mista Oseloka Obaze, dan takara na PDP a zaben Anambra

Ya ce ko da yake ya gabatar da wata sanarwa da ta yi watsi da sakamakon zaben bayan INEC ta sanar, amma yanzu ba shi da niyyar jayayya da wannan tsari.

KU KARANTA: Gwamna Fayose na kokarin tserewa daga PDP – Sanata Aluko

Obaze ya ce: "Na taya gwamna Willie Obiano da mataimakinsa, Dakta Nam Okeke murna a kan nasarar da suka yi a zaben gwamna na Anambra wanda aka yi a ranar 18 ga Nuwamba 18, ina wa mutanen biyu fatan alheri”.

Idan dai baku manta ba a safiyar yau Litinin ne Legit.ng ta ruwaito cewa Obaze ya ki amince da sakamakon zaben a ranar Asabar, yayin da ya yi zargin cewa an tafka magudi da rashin daidaito.

Obaze ya yi amfani da damar wajen mika gaisuwar ta’aziyarsa zuwa ga iyalan marigayi tsohon mataimakin shugaban kasar, Cif Alex Ekwueme, wanda Allah ya yiwa rasuwa a Landan a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel