An yabawa Shugaba Buhari game da gudanar da zaben Anambra

An yabawa Shugaba Buhari game da gudanar da zaben Anambra

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha jinjina daga Jama’a

- An gudanar da zaben Anambra cikin zaman lafiya makon nan

- Buhari yayi wa Gwamna alkawarin yin zabe mai inganci a Jihar

Labari ya kai gare mu cewa an yabawa Shugaban Kasa Buhari game da gudanar da zaben Jihar Anambra da aka yi a karshen wannan makon. Dama can Shugaba Buhari yayi wa Gwamna Obiano alkawarin yin zabe na gari.

An yabawa Shugaba Buhari game da gudanar da zaben Anambra

Shugaba Buhari tare da Obiano kafin zaben Anambra

‘Yan Siyasar Kasar daga Jam’iyyu da dama sun jinjinawa Shugaba Buhari da Hukumar zabe na kasa watau INEC wajen kokarin su na aikin zaben da Gwamna mai-ci Willie Obiano ya lashe inda zai zarce zuwa 2021.

KU KARANTA: Buhari ya aikawa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan sako na murna

Har irin su Gwamna Ayo Fayose da yana cikin manyan ‘Yan adawar kasar ya yabawa zaben da aka gudanar. ‘Yan Jam’iyyar APGA sun bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika mutum mai adalci.

Har wa yau sauran Jam’iyyu da su ka sha kashi har da Jam’iyyar APC mai mulkin kasar sun yarda da sakamakon zaben. Irin su Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ma dai ya jinjinawa Shugaban Kasar. PDP ta zo na uku a zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel