Ta'addanci: Mayakan Boko Haram sun fille kan wasu manoma 6 a Borno

Ta'addanci: Mayakan Boko Haram sun fille kan wasu manoma 6 a Borno

- Kungiyar Boko Haram ta kashe wasu manoma 6 a yankin karamar hukumar Mafa a jihar Borno

- Mayakan sun fille kan manoman yayin da suke aiki a gonakinsu

- Wani memba na ‘yan yakin sa kai ya ce 'yan bindigar sun kai harin ne a saman babura

Kungiyar Boko Haram ta fille kan wasu manoma shida a garin Dimge da ke yankin karamar hukumar Mafa a jihar Borno.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewa wannan danye aiki ne mafi girma a hare-hare na kwanan nan da mayakan suka kai a arewa maso gabashin kasar, inda aka kashe mutane fiye da 20,000 a cikin shekaru 9 na hare-haren ta’adanci a yankin.

Wannan kisan ta faru ne a ranar 19 ga Nuwamba, yayin da manoma ke aiki a gonakin su, wani wanda lamarin ya fari a idon sa, Jiddah Ahmad, ya shaida wa jaridar NAN a garin Jere kusa da Maiduguri ranar Litinin.

Boko Haram: Mayakan Boko Haram sun fille kan wasu manoma 6 a Borno

‘Yan yakin sa kai a yankin arewa maso gabas

Ahmad ya ce, 'yan bindiga sun sace manoma 7 a lokacin da suke aiki a gonakinsu kuma suka kashe 6 daga cikin su a wani daji kusa da gonakin.

KU KARANTA: Yan fashi da makami sun dira wata kasuwa a jihar Kastina, sun hallaka jama’a da dama

Ahmad, wanda ya kasance dan uwan daya daga cikin manoman da aka kashe, ya ce manoma 2 cikin wadanda aka kashe sun fito ne daga kauyen Lawanti Gongulon dake Jere.

A cewarsa, sauran manoma 4 sun fito daga kauyen Masu wanda ke karamar hukumar Mafa na jihar.

Wani memba na ‘yan yakin sa kai, Usman Muhammad, ya shaidawa NAN cewa 'yan bindiga sun kashe wasu manoma 4 a wannan wurin a baya.

Muhammadu ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kai farmaki ga manoman ne a saman babura.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel