Gwamna Fayose na kokarin tserewa daga PDP – Sanata Aluko

Gwamna Fayose na kokarin tserewa daga PDP – Sanata Aluko

- Akwai kishin-kishin din cewa Fayose na neman barin PDP

- Gwamnan Ekitin na kokarin tserewa zuwa APC mai mulki

- Wani Sanata yace Ayo Fayose na shirin sulalewa zuwa APC

Kwanan nan wani labari ya kai gare mu daga Jaridar Daily Post cewa Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose na kokarin tserewa daga PDP zuwa APC.

Gwamna Fayose na kokarin tserewa daga PDP – Sanata Aluko

Ayo Fayose na Jihar Ekiti na neman barin PDP

Wani tsohon babban Sanata a Kasar watau Gbenga Aluko ya fasa wannan kwan inda yace Gwamnan yana kokarin dawowa Jam’iyyar APC mai mulki a yayin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Jihar Ekiti na Ado-Ekiti.

KU KARANTA: Kashamu ya soki Makarfi game da zaben Jihar Anambra

Sanata Gbenga Aluko wanda ya wakilce Kudancin Jihar Ekiti tun a 1999 zuwa 2003 yace Gwamna Fayose ya lura cewa PDP ba za ta cigaba da kai labari ba don haka yake kokarin sulalewa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki a kasar.

Aluko yayi kaca-kaca da Fayose wanda yace ba zai iya cin mulki ba tare da karfin Gwamnatin Tarayya ba. Tsohon Sanatan yace duk motsin da Ayo Fayose yayi dai kar yake kallon sa kuma zai sha mamaki a zaben 2018 na Jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel