APC ta jinjina wa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan

APC ta jinjina wa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan

- Jam’iyyar APC ta jinjinawa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan yayin cika shekaru 60 da haihuwa

- Jam’iyyar ta bukaci Jonathan ya ci gaba da manufofinsa na kwarai don ci gaban al’ummar kasar

- APC ta bukaci Jonathan ya ci gaba da tallafawa ci gaban Najeriya

Jam'iyya mai mulki ta APC ta taya tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan murnar jika shekaru 60 da haihuwa, yayin da ta bayyana shi a matsayin shugaban kwarai da kuma na gari.

A wata sanarwa da sakataren hulda da jama’a, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya hannu, ta bukaci Jonathan ya ci gaba da manufofinsa na kwarai don ci gaba da neman zaman lafiyar kasa.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, jam'iyyar ta ce ta tuna da jaruntakar tsohon shugaba Goodluck Jonathan gabani da zaben shugaban kasa na shekara ta 2015 da kuma bayan zaben, wanda ya nuna ƙaunarsa ga Najeriya.

APC ta jinjina wa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

APC ta bukaci Jonathan ya ci gaba da tallafawa ci gaban kasar.

KU KARANTA: Jonathan ya mayar da martani game da zargin tattara naira biliyan 5 daga asusun fensho

A ranar lahadi, 19 ga watan Nuwamba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aika sakon taya tsohon shugaba Jonathan murnar cika shekaru 60 da haihuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel