Sakkwato: Kada ka yi wasa da wuta - 'Yan Shi'a sun gargadi Tambuwal

Sakkwato: Kada ka yi wasa da wuta - 'Yan Shi'a sun gargadi Tambuwal

- Kungiyar ‘yan Shi'a ta gargadi gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal akan cin zarafin ‘ya’yanta

- Kungiyar ta ce tana da labari Tambuwal na shirin cin zarafin mambobin IMN a jihar Sakkwato

- IMN tace za ta tuhumi Tambuwal da alhakin duk wani hari a kan mambobin ta

Kungiyar ‘yan Shi'a, IMN ta gargadi gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal cewa kada ya kuskura ya dauki wani matakin da zai takura wa kungiyar a jihar.

Daraktan labarai na hukumar, Ibrahim Musa, ya ba da wannan gargadin a wata sanarwa a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Ya ce kungiyar na da labarin cewa Tambuwal na shirin cin zarafin IMN da mambobinsa a jihar Sakkwato.

Sakkwato: Kada ka yi wasa da wuta - 'Yan Shi'a sun gargadi Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal

Musa ya yi zargin cewa shirin ya hada da kashe ‘ya’yan kungiyar da dama, ciki har da mata da yara, da kuma lalata dukiyar da za su hada da gidaje da wuraren kasuwanci.

KU KARANTA: Yanayin shugabancin El-Rufai ya haifar da APC akida - Hakeem Baba Ahmed

"A yayin shirya wannan shiri, an gudanar da taro na asirce nan gida da kuma wajen jihar , inda masu halartar tarurruka suka yanke shawarar cewa gwamna zai iya samun wa’adi na biyu a ofis ne kawai idan gwamnati ta aiwatar da wannan mumunar shiri ga ‘yan Shi’a ", inji shi.

"A makon da ya wuce ne wani kungiyar Al’ummar Mabera Magaji watau ‘Mabera Magaji Community’ ta ta rubuta takarda ga kwamishinan 'yan sandan jihar inda ta bukaci a rushe gidan shugaban IMN , ko sake masa masuguni cewa makwabcin shugaban suna cikin fargaba”.

"Saboda haka ya kamata gwamna Tambuwal ya bi a hankali. Zamu tuhume shi da alhakin duk wani hari a kan mambobin IMN da shugabannin ta da kuma dukiyoyi a jihar Sakkwato”.

"A karshe, mun yi kira ga gwamnan Tambuwal ya ba da damar samun zaman lafiya a jihar ya kuma ba dukkan 'yan kasa damar samun' yanci kamar yadda tsarin mulki ta tabattar. A matsayinsa lauya, muna fatan zai girmama wannan bangare na dokokin kasar".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel