Tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari yayi jimamin mutuwar tsohon mataimakinsa

Tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari yayi jimamin mutuwar tsohon mataimakinsa

- Turakin Sakkwato, ALhaji Shehu Shagari yayi jimamin rasuwar Alex Ewkwueme

- Alex Ekwueme ya rasu a ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba a Landan

Tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari ya jajanta ma yan Najeriya biyo bayan mutuwar Cif Alex Ekweme, tsohon mataimaikin shugaban kasa a zamanin Shagari, daga shekarar 1979-1983.

Daily Trust ta ruwaito Shagari ya bayyana haka ne cikin wata gajeruwar sanarwa, wanda ta samu sa hannunsa a garin Sakkawato, inda yace:

KU KARANTA: Yan fashi da makami sun dira wata kasuwa a jihar Kastina, sun hallaka jama’a da dama

“Na kadu bayan samun labarin rasuwar dan uwana, koma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alex Ekwueme. Alex mutum ne wanda ke da Kankan da kai, kuma bai biyayya matuka. A madadi na, ina jajanta ma yan Najeriya, da fatan zai samu hutu a rayuwar barzahu.” Inji Turakin Sakkawato.

Tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari yayi jimamin mutuwar tsohon mataimakinsa

Shehu Shagari

Legit.ng ta ruwaito a satukan da suka gabata ne dai ciwon Alex ya tashi, inda gwamnatin tarayya ta umarci ta dauki nauyin garzaywa da shi wani asibiti a Landan don samun kulawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel