Buhari yayi bakin ciki kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Ekwueme

Buhari yayi bakin ciki kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Ekwueme

Shugaba Muhammadu Buhari yayi jaje ga yan Najeriya, da gwamnatin jihar Anambra da mutanenta, kan rashin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alex Ifeanyichukwu Ekwueme (GCON), a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba, 2017.

Shugaba Buhari yana jaje ga dukkan mutanen masarautar Oko, majalisar sarautan Aguata, da iyalen Ekwueme, bisa rashinsa da suka yi, wanda za’a yi rashi sosai a fannin shawarwarin sa kan al’amuran kasa da zaman lafiyar kasa.

Shugaban kasar ya nuna tabbacin cewa jajircin Dr Ekwueme ga hadin kan Najeriya ya karfafa gwiwan gwamnatoci da dama, shugaban ya tuno da hadaya da marigayin yayi musamman wajen ganin an gina dawwamammiyar mulkin demokradiyya a Najeriya.

Buhari yayi bakin ciki kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Ekwueme

Buhari yayi bakin ciki kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Ekwueme

KU KARANTA KUMA: Yan majalisa 2 kacal da PDP ke dasu a jihar Nasarawa zasu sauya sheka zuwa APC – Kakakin majalisa

Shugaba Buhari ya yarda cewa Dr Ekwueme yayi aiki gwargwadon hali don inganta rayuwar talakawa da wadanda basu samu damar more rayuwa ba ta shirin Alex Ekwueme Foundation, shugaban ya bayyana shi a matsayin mutum da ya bauta wa kasarsa da kuma al’umma.

Shugaban yayi addu’a cewa Allah jikan tsohon mataimakin shugaban kasar, Allah kuma ya kara wa iyalensa hakuri kan rashin da suka yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel