Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya fasa zuwa Kano

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya fasa zuwa Kano

Rahoto dake zuwa mana ya nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai samu damar zuwa jihar Kano kamar yadda aka shirya a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba ba.

Jaridar Rariya ta ruwaito hakan daga makusancin shugaban kasar.

Zuwan shugaba Buhari jihar Kano abu ne da ke tayar da kura a siyasar jihar Kano, yayinda da wasu ke korafin cewa ya kauracewa jihar Kano da ta fi kowacce jiha ba shi zunzurutun kuri'a gami da yi masa addu'ar samun lafiya.

Wasu kuma na hasashen ya kauracewa jihar ne saboda gudun ruruta wutar rikicin da ke tafarfasa tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso.

KU KARANTA KUMA: An bai wa Mugabe wa'adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Majiyar ta kara da cewa, ana sa ran sai ranar 6 ga watan Disamba shugaba Buhari zai kai ziyara jihar.

Kusan wannan shine karo na biyu da aka daga zuwan shugaban kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel