Yan sara-suka sun kashe shugaban kungiyar yan banga a Jos

Yan sara-suka sun kashe shugaban kungiyar yan banga a Jos

Yan sara suka sun daba ma wani mataimakin shugaban yan banga mai kula da sashin Sarkin Arab a karamar hukumarJos North dake jihar filato wuka har lahira a safiyar jiya Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.

Yan sanda sun tafi da gawar shugaban yan bangan mai suna Musa Jalo, wanda aka fi sani da Baba Musa, inda daga baya suka saki gawar ga iyalen marigayin don binnewa.

Kwamanda dake ai kula da jin dadin kungiyar yan bangan Najeriya (VGN) a jihar, Ahmad Mudi, wanda ya tabbatar da aukuwar al’amarin a wayar talho, ya ce “yan sara suka biyu ne suka kai mishi hari yayinda yake dawowa daga West of Mines tare da abokinsa da misalign karfe sha biyu na dare.”

Mudi ya ce yan sara sukan sun bi marigayin inda suka kira sunana shi kafin suka daba mishi wuka sau biyu a wuya da kuma baya.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi bakin ciki kan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa Ekwueme

Ya ce abokin marigayin ne ya kira yan sanda cikin gaggawa don tafiya das hi asibiti inda aka tabbatar ya mutu.

“Wannan shine mamba na hudu da yan daba suka kashe cikin shekeran nan a jihar.

"An kashe daya a karamar hukumar Wase, biyu kuma a Qua’an Pan yanzu kuma a Jos North. Muna tsammanin cewa gwamnatin jihan zata dauki mataki kan yanda muke saka rayukanmu a hatsari don kare al’umma,” a cewar shi.

A lokacin da aka tuntube shi, mai Magana da yawun rundunar yan sandan sashin jihar Filato, ASP Tyopev Terna, ya ce bai sami DPO dake kula da yankin ba a wayar talho, wannan ne yasa bai bada jawabi ba kan al’amarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel