Zaben Anambara : Atiku yayi magana akan nasarar da Obiano ya samu

Zaben Anambara : Atiku yayi magana akan nasarar da Obiano ya samu

- Atiku Abubkara ya taya mutanen jihar Anambara murna akan zaben da aka gudanr a ranar Asabar a cikin lumana

- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya yayi kira da wadanda suka fadi a zaben, da hada hanu da gwamanan wajen kawo wa jihar cigaba

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar yayi tsokaci akan sakamakon zaben gwamnan jihar Anambara da aka gudanar a rana Asabar 18 ga watan Nawumba.

Gwamnan Willei Obiano ya kara lashe zaben gwamnan jihar Anambara da aka gudanar.

Obiano wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, ya yiwa dan takarar jam’iyyar APC da na PDP fice da kuri’u sama da dubu dari.

Zaben Anambara : Atiku yayi magana akan nasarar da Obiano ya samu

Zaben Anambara : Atiku yayi magana akan nasarar da Obiano ya samu

Atiku ya ce tabbas Obiano ne ya lashe zaben Anambra.

KU KARANTA : Bankin Duniya ta amince ta ba El-Rufai bashin Dala miliyan $350

Atiku ya taya mutanen jihar Anambara murnar a shafin sa na tuwita akan zaben da aka gudanar a cikin lumana.

“Wanda suka samu nasarar a wannan zabe sun mutanen jihar Anambara. Kuma ina kira da wadanda suka fadi su hada hanun da kafe wajen kawo ma jihar cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

https://youtu.be/jjdZGSqcWEQ

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel