An gurfanar da uban da ya tunzura dansa wasa da maciji da ya yi ajalinsa a jihar Katsina

An gurfanar da uban da ya tunzura dansa wasa da maciji da ya yi ajalinsa a jihar Katsina

Rahotanni sun kawo cewa an gurfanar da wani uba mai bada kafiyar maciji da aka ambata da suna Isah Saidu a gaban kotun majistare dake jihar Katsina.

An gurfanar da magidancin ne akan zargin yin sanadiyar mutuwar dansa mai shekaru 15 a duniya sakamakon tursasa yaron yin wasa da maciji baá son ransa ba.

Wannan al’amari ya afku ne a ranar 5 ga watan Nuwamba a kauyen Kuringata dake karamar hukumar Kafur na jihar Katsina inda Saidu ya tursasa yaronsa yin wasa da macijin da ya sare shi wanda ya kuma yi sanadiyyar mutuwar yaron kamar yadda dansandan da ya shigar da karar ya bayyanawa kotun.

Yaron dai ya rasu ne awanni kadan bayan an kai shi babban asibitin dake karamar hukumar Malumfashi sakamakon dafin macijin a jihar.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya taya Jonathan murnar cika shekaru 60 a Duniya

Kotun a karkashin mai shara’ar Hajiya Fadila Dikko ta dage karar zuwa 19 ga watan Disamba game da wasu bincike da ‘yan sanda ke cigaba da yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel