Nigerian news All categories All tags
Yan sanda sun bankawa matatun man fetur 40 wuta a Edo

Yan sanda sun bankawa matatun man fetur 40 wuta a Edo

Rundunar yan sandan jihar Edo ta sanar da cewar ta tayar da matatun man fetur guda 40 wanda aka kafa su ba’a bisa ka’ida ba wuta a dajin Egono dake karamar hukumar Estako na jihar.

A lokacin da yan sanda ke nemen mafakar yan fashi da makami tare da masu garkuwa ne suka gano wadannan matatun man. Matatun man fetur din da aka gano sun kasance na wasu mutane daban-daban.

Hasashe sun nuna cewa an fasa bututun man fetur din da ya ratsa cikin kauyen a yayin da wadanda ake zargi suka sanya na su bututun daga cikin bututun kamfanin NNPC don su jawo man fetur din.

Yan sanda sun bankawa matatun man fetur 40 wuta a Edo

Yan sanda sun bankawa matatun man fetur 40 wuta a Edo

Don abun ya masu sauki, masu matatun sun gina ramuka da dama inda a ciki ne suke ajiye man fetur din da suka tace kafin su zuba shi cikin gangan mai ko galan.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya taya Jonathan murnar cika shekaru 60 a Duniya

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, Johnson Babatunde Kokumo, ya ziyarci inda aka gano matatun mai fetur, inda ya ce yin hakan na haddasa ma kasar yin babban hassara.

Ya kara da cewa an kama mutane 6 a wajen, tare da mamakin yadda jami’an tsaro suka kasa gano mutanen ba na tsawon shekaru da dama. Ya ce sun tuntube jami’an NNPC sannan kuma an gyara bututun man.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel