Zaben Anambara: Babu wani abun mamaki a nasarar da Obiano ya samu – Shugaban jam’iyyar APGA, Oye

Zaben Anambara: Babu wani abun mamaki a nasarar da Obiano ya samu – Shugaban jam’iyyar APGA, Oye

- Cif Victor Oye ya ce nasarar Obiano a zaben Anamabara bai bashi mamaki ba

- Shugaban APGA ya ce Ubangiji da kokarin Obiano yasa ya samu nasara a zaben Anambara

- Kyawawan halayen Obiano yasa jam’iyyar APGA ta samu nasara

Shugaban jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Victor Oye, yace nasarar da Gwamna Willie Obiano ya samu a zaben gwamnan jihar Anambara da aka kammala bai bashi mamaki ba.

Cif VictorOye ya bayyana haka ne a jiya lahadi bayan hukumar zabe na INEC ta sanar da sakamakon zaben a Awka.

Zaben Anambara : Babu wani abun mamaki a nasarar da Obiano ya samu – Shugaban jam’iyyar APGA, Oye

Zaben Anambara : Babu wani abun mamaki a nasarar da Obiano ya samu – Shugaban jam’iyyar APGA, Oye

Shugaban APGA ya ce Ubangiji da kokarin Cif Willei Obiano ya sa ya samu nasara a zaben gwamnan jihar.

KU KARANTA : Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

Kyawawan halayen Obiano yasa jam’iyyar APGA ta samu nasara a zaben Anambara.

Ban ta ba samun shakku zuciyata ba cewa wata wani jam’iyya zata iya kwace mulki daga hanun jam’iyyar APGA a Anambara.

Obiano yayi kokari a fannin tsaro, ilimi da tattalin arziki a jihar Anambara, babu jihar da ta kai Anambara zaman lafiya a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel