Nigerian news All categories All tags
Yan fashi da makami sun dira wata kasuwa a jihar Kastina, sun hallaka jama’a da dama

Yan fashi da makami sun dira wata kasuwa a jihar Kastina, sun hallaka jama’a da dama

Wasu gagararrun yan fashi sun kai hari a wata kasuwar hatsi dake garin Sheme, bayan sun tare hanyar Kankara zuwa Sheme, tare da yin harbin mai kan uwa da wabi akan motocin dake tahowa.

Daily Trust ta ruwaito wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yaga gawar wasu mata biyu da karamin yaro akan babban titin, tare da wasu mutane da dama da suka samu rauni daban daban.

KU KARANTA: Ta hallaka mijinta, yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta hanyar caka masa wuƙa a Al’auransa

Haka zalika, wani mutum mai suna Umar Kado ya bayyana cewa yayarsa mai suna Talatu Muhammed tare da jaririnta na daga cikin wadanda suka rasu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Yan fashi da makami sun dira wata kasuwa a jihar Kastina, sun hallaka jama’a da dama

Yan fashi da makami

“A lokacin da muka je dauko gawarta, sai muka hadu da wasu mutane daga Zamfara, suma sun zo daukan gawarwakin yan uwansu guda biyu da suka mutu a harin.” Inji Kado.

Kado ya kara da cewa ya ga wani direban mota daya samu mummunan rauni a kafa. “ Ina tsammanin sun harbi motar direban ne, kuma na samu labarin sama da mutane 10 sun mutu a sakamakon harin da aka kai ma Motoci kadai.”

Sai dai da aka tuntubi Kaakakin Yansandan jihar, DSP Gambo Isah don jin ta bakinsa, sai ya nuna bashi da masaniya dangane da lamarin, amma zai bincika.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel