Zaben 2019 : Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan – Ayo Fayose

Zaben 2019 : Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan – Ayo Fayose

- Dan takarar Gwamnan Ekiti a jam'iyyar APC ya zargi Faysoe da yunkurin canza sheka zuwa APC

- Fayose ya karyata zargin da ake masa na yunkurin canza sheka zuwa jam'iyyar APC

- Gwaman Ekiti ya ce shiga jam'iyyar APC kamar bin hanyar shaidan ne

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya mayar da martani akan zargin da dan takarar gwamnan jihar Ekiti a jam’iyyar APC Gbenga Aluko yayi masa na cewa, Fayose yana yunkurin canza sheka zuwa APC.

Gbenga Aloku, tsohon mataimakin Cif Wif na majalissar dokoki, ya zargi Fayose da yunkurin dawowa jam’iyyar APC saboda yana ganin PDP ba zata iya cin zaben da za a gudanar na ga ba.

Zaben 2019 : Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan – Ayo Fayose

Zaben 2019 : Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan – Ayo Fayose

A jawabin da Fayose ya fitar a ranar Lahadi ta magana da yawun bakin sa, Idowu Adelusi, Fayose yace “Shiga jam’yyar APC kamar mutum ne ya ba hanyar Yesu almasihu, ya bi hanyar shaidan".

KU KARANTA : Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Zargin da ake wa Fayose na yunkurin canza sheka zuwa APC karya ce.

Fayose ba zai taba shiga jam’iyyar APC ba, sai dai ya yayi maraba da yan APC da za su dawo PDP A jihar Ekiti,

“Yanzu haka Fayose yana shire-shiryen yadda mika mulki zuwa ga magajin sa wanda zai fito a jam’iyyar PDP a 2019."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel