Nigerian news All categories All tags
Neman kudin aure: Wani Matashi yayi garkuwa da budurwarsa, da nufin amsan kudin fansa

Neman kudin aure: Wani Matashi yayi garkuwa da budurwarsa, da nufin amsan kudin fansa

Rundunar Yansandan jihar Edo ta cika hannu da wani Saurayi mai suna Michael Dodo, wanda ake zargi da satar wata yarinya mai shekaru 16, tare da yin garkuwa da ita, a wani salo na satar mutane.

Daily Trust ta ruwaito Dodo na daya daga cikin miyagun mutanen masu aikata manya laifuka su 104 da rundunar ta kama, kuma kwamishinan Yansandan jihar Babatunde Johnson Kokuma yayi bajakolinsu.

KU KARANTA: Ta hallaka mijinta, yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta hanyar caka masa wuƙa a Al’auransa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dodo ya hadu da yarinyar ne a shafin sadarwar zamani, Facebook, inda ya gayyace ta zuwa gidansa, a haka ne yayi garkuwa da ita, kuma ya bukaci a biya fansan naira miliyan hudu.

Sia dai dayake yi ma yan jaridu karin haske, Dodo yace “A Facebook muka hadu da ita, kuma ina matukar kaunarta, don haka nake son na aureta, amma bani da kudi, dalilin da yasa kenan na shirya sace ta, don na samu kudin aurenta daga kudin fansan da za’a biya.”

A wani labari na daban kuma, yarinyar ya bayyana cewa bayan da Dodo ya sace ta, sai daya kwashe kwanaki hudu yana yi mata fyade, kafin daga bisani ya nemi a biya shi kudin fansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel