Kasafin 2018: Buhari ya ware Naira miliyan 158 don sayen man janareta a ma'aikatar wuta

Kasafin 2018: Buhari ya ware Naira miliyan 158 don sayen man janareta a ma'aikatar wuta

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta kasafta akalla Naira miliyan 158 domin sayen man janaretocin su da kuma sauran gyare-gyare a ma'aikatar wutar lantarki, manyan ayyuka da gidaje a shekara mai zuwa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin kasafin kudin shekarar mai kamawa da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban majalisar tarayyar a farkon watan nan domin su amince da shi.

Kasafin 2018: Buhari ya ware Naira miliyan 158 don sayen man janareta a ma'aikatar wuta

Kasafin 2018: Buhari ya ware Naira miliyan 158 don sayen man janareta a ma'aikatar wuta

KU KARANTA: Wasu 'yan APC na yiwa Buhari zagon kasa - Masari

Legit.ng dai ta samu cewa kusan dukkan kananan ma'aikatu da kuma sannan mulki dake karkashin babbar ma'aikatar ta wuta da sauran manyan ayyuka sun bukaci miliyoyin Nairori ne domin sanyawa janaretocin su mai a shekarar mai kamawa ta 2018.

Wannan dai na zuwa ne duk kuwa da irin dumbin alkawurran da gwamnatin nan ke yi a game da gyaran wutar kasar da a halin yanzu ya lakume dubban biliyoyin daloli.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel