Zaben 2019 : Ya kamata Buhari ya je gida ya huta - Sanata El-Jibrin Dogowa

Zaben 2019 : Ya kamata Buhari ya je gida ya huta - Sanata El-Jibrin Dogowa

- El-Jibrin Dogowa ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari kada ya kara tsayawa takara a zaben 2019

- Doguwa ya ce rashin lafiyar Buhari ya hana shi shawo kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta

- Tsohon dan majalissar ya ce rashin iya shugabancin wannan gwamnatin ya shafe shi

Shugaban jam’iyyar PDP na farko a jihar Kano Mas’ud El-Jibrin Dogowa ya shawarci shugaban kasa Muhammadi Buhari ka da ya kara tsaya takara a zaben 2019.

Dogouwa wanda ya wakilci mazabar Arewacin Kano a majalissar Wakilai, ya ce kasar na fuskantar karancin tsaro da koma bayan tattalin arziki, kuma Buhari ya kasa shawo kan matsalolin saboda rashin lafiyar jikin sa.

Zaben 2019 : Ya kamata Buhari ya je gida ya huta - Senata El-Jibrin Dogowa

Zaben 2019 : Ya kamata Buhari ya je gida ya huta - Senata El-Jibrin Dogowa

A zanatwar da yayi da yan jaridar SUN a karshen makon da yagabata, Mas’ud El-Jibrin Dogowa ya ce Buhari ya je gida ya huta.

KU KARANTA : Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

“Ina magana ne a matsayi na na dan Najeriya da rashin iya shugabancin gwamnatin nan ya shafe ni.

“Idan ka kalla rashin tsaro, da yadda kawunan al’ummar Najeriya ya kara rabuwa

“Idan kalla yadda yan Najeriya ke shan wahala, da rashin aikin yi yayi katutu a ko ina a fain kasar, za k ace Buhari ya je gida ya huta.

“Ya je gida ya huta dan kula da lafiyar jikin sa”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel