Mugabe ya ƙeƙashe ƙasa, ya tubure, ba zai sauka daga kujerar shugaban kasa ba

Mugabe ya ƙeƙashe ƙasa, ya tubure, ba zai sauka daga kujerar shugaban kasa ba

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya tabbatar ma yan kasar cewa ba zai yi murabus ba, wani lamari daya baiwa yan kasar mamaki, kuma suka shiga dimuwa.

Da fari dai BBC ta ruwaito wakilinta dake kasar, Fergal Keane ya shaida mata cewa saura kiris ya rage shugaba Mugabe yayi murabus, amma sai ga shi an samu akasin haka.

KU KARANTA: Ta hallaka mijinta, yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta hanyar caka masa wuƙa a Al’auransa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mugabe ya shaida ma yan kasar haka ne a wata sanarwa da yayi da kansa kai tsaye daga fadar gwamnatin kasar, tare da shuwagabannin Sojojin kasar da kuma jami’an sulhu da suka zo daga kasar Afirka ta kudu.

Mugabe ya ƙeƙashe ƙasa, ya tubure, ba zai sauka daga kujerar shugaban kasa ba

Mugabe

Mugabe dai ya fara jawabin nasa ne da godiya ga rundunar Sojin kasar, inda ya yaba ma kokarinsu na ceto kasar, “A matsayin na babban kwamandan Sojin kasar Zimbabwe, na gamsu da bayanan matsalolin da suka janyi hankali na akan su.

“Aikin da Sojojin suka yi wanda yayi kama da juyin mulki ba juyin mulki bane, kuma bai saba ma doka ba, babban matsalar mu ita ce rarrabuwan kai da aka samu tsakanin jam’iyar mu da gwamnati, shine wasu ke ganin ya dauke hankalinmu daga gyaran tattalin arzikin kasa.”

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mugabe ya cigaba da bayyana kokarin da Sojojin kasar tare da sauran jama’a suka yi na ganin an kwato ma kasar yancin kanta a baya, rahotanni sun nuna cewa daga cikin abin da ya kawo rabuwan kai shine rashin ganin muhimmancin mazan jiya da matar Mugabe, Grace, ta daura shi akai.

Daga karshe, yayi alwashin aiwatar da duk gyare gyaren da aka lurar da shi, musamman na janyo wadanda suka sha gwagwarmayan neman yancin kai a jiki, tare da tabbatar da ladabtarwa a jam’iyyar ZANU-PF.

Sai dai an ruwaito wasu jama’an kasar da dama da suka kalli jawabin shugaban kasa sun shiga cikin damuwa, sakamakon rashin murabus dinsa, inda wasu ma an ruwaito sun sha kuka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel