Wani Farfesa ya binciko cutar dake sanya shuwagabannin Najeriya wawushe kuɗin kasar

Wani Farfesa ya binciko cutar dake sanya shuwagabannin Najeriya wawushe kuɗin kasar

Wani hamshakin masanin yanayin dan adam, kuma likitan mahaukata, Farfesa Franzek ya bayyana cewa wani nau’in hauka ne ke sanya shuwagabannin Najeriya dabi’an satar kudaden al’umma.

Farfesa Franzek wanda ya kwashe shekaru 40 yana bincike a fannin hankali da kwalkwalr dan Adam an haife shi ne a kasar jamus, kuma yayi karatu a Jamus, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Ta hallaka mijinta, yaron tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta hanyar caka masa wuƙa a Al’auransa

Dayake amsa akan menene dalilin da yasa shuwagabannin Najeriya ke sata, sai yace, “Attajirai a Najeriya suna samun kudi, amma kwakwalrsu ta mutu, su kuma talakawan basa iya furta ra’ayinsu har yayi tasiri.”

Farfesa ya kara da cewa wannan matsalar nada nasaba da yanayin da yan Najeriya ke girma a ciki, inda yace inda ace shuwagabannin Najeriya na samun tarbiyya yadda ya kamata, kuma ace sun girma cikin yanayi mai kyau, toh da basu saci kudaden jama’a ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesa Franzek yana fadin idan yaro tun yana karami ya saba da cewa sai ya wahala kafin ya samu abincin da zai ci, ko kuma sai ya nema da kansa, sakamakon iyayensa basu da halin bashi kudi, toh dole irin wannan yaro yayi sata idan ya zama shugaba, saboda kwakwalwar sa ta saba da haka.

Wannan cuta dai sunan ta a turance ‘Kleptomania’, wanda bata barin ya samu kwanciyar hankali muddin bai sata kayan mutane ba.

Farfesa ya bada shawarar yadda za’a sauya al’amarin, inda yace “Ya zama wajibi yan Najeriya su fara zaben shuwagabannin masu kyawawan manufofi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel