Yanayin shugabancin El-Rufai ya haifar da APC akida - Hakeem Baba Ahmed

Yanayin shugabancin El-Rufai ya haifar da APC akida - Hakeem Baba Ahmed

- Baba Ahmed ya ce APC akida ba sabuwar jam'iyya ba ne

- APC akida kugngiyar mutanen da ba sa jin dadin yanayin shugabancin gwaman jihar Kaduna

- Hakeem ya nuna rashin goyoyn bayan koran mallamai 21,000 da gwamnatin jihar Kaduna ke kokarin yi

Tsohon shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na jihar Kaduna, Dakta Hakeem Baba Ahmed yace yanayin shugabancin Nasir Ahmed el-Rufai ya haifar da APC akida.

Hakeem wanda ya kasance shugaban hadiman shugaban majalissar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya ce APC akida ba sabuwar jam’iyya ba ne, kungiyan wasu mutane ne a cikin APC da ba su amince da yadda gwamnan jihar yake gudanar da shugabanci a jihar ba.

Dakta Hakeem Baba Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da yan jarida a Kaduna.

Yanayin shugabancin El-Rufai ya haifar da APC akida - Hakeem Baba Ahmed

Yanayin shugabancin El-Rufai ya haifar da APC akida - Hakeem Baba Ahmed

Manufar APC akida shine tabbatar da bin ka’odojin jam’iyyar APC a jihar Kaduna. Saboda a yanzu haka gwamna Nasiru El-Rufai yana rusa jam’iyyar ne.

KU KARANTA : Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Hakeem ya nuna rashin goyon bayan koran mallamai 21,000 da El-Rufai yake kokarin yi a jihar Kaduna.

Baba Ahmede ya karyata goyon bayan korar mallam makaranta 21,000 da ake ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, ya ce shugaban kasa ya goyi bayan gyara fannin ilimi ba koran mallamai daga bakin aikin su ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel