Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

- Kungiyar PLAC ta ce Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

- Daraektan kungiyar ya ce jam’iyyun suna ta amfani da dabaru daban-daban suna sayan kuri’on wadanda suka zo yin zabe

Kungiyar PLAC ta kwatanta zaben gwamnan jihar Anambara da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Nawumba a matsayin mafi muni zabe tun lokacin da mulkin dimokadiyya ya dawo Najeriya tun shekara 1999.

Darektan Hukumar PLAC Clement Nwankwo, ya bayyana haka ne a zantawar da yayi da yan jarida a Awka babban birnin Anambara.

Ya ce "jam’iyyun suna ta amfani da dabarun daban-daban suna sayan kuri’on wadanda suka zo kada zabe.

Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

Zaben gwamnan jihar Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999

“Ana sayan kuri’a daya a farashin naira N500 zuwa N5,000.

KU KARANTA : Hoton dansandan Najeriya a shagon welda yana gyara bindigan sa

Nwaknwo yace "bincike ya nuna cewa ba a biya ma’aikatan gudanar da zaben ba, tare da masu bautan kasa da aka dauka dan taimakawa wajen gudanar da zaben.

"Ba a biya yansanda kudin sayan abinci ba, wasu sunyi kwana daya ba su ci abinci ba . Ba daice ba, a bar mutanen dake cikin irin wannan yanayi su kasance a cikin masu gudanar da zabe".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel