Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai na Najeriya, wato Atheist Society of Nigeria, kungiya ta wadanda suke kiran addinai da sunan chamfi, sun hada da dalibai wadanda suka baro addinai daban-daban, suka kuma karyata samuwar alloli, kuma suka rungumi ihsani da kimiyya a matsayin sabuwar hanyar rayuwa, sun yi taro a Jami'ar Legas a bana.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

A taron nasu dai, sun karbi bakuncin baki daga kasashe makwabta, kamar Ghana da Kenya, Ingila da Jamus, daga kungiyoyi takwaorinta ya wadannan yankunan, wadanda tuni sun yi nisa a irin wannan turba ta son ilmi da zaman lafiya.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Taron ya hado kan dalibai daga sassa daban daban na kasa, samari da 'yan mata, wadanda bisa irin nasu dalilan, suke ganin basu gamsu da yadda addinai ke bayani da mulkar rayuwar jama'a ba.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Masu jawabi a taron, sun bayyana hanyoyi da suka bi suka fahimci rayuwa da ci gaban da kungiyar tasu ta samu musamman rajistar kungoyoyin a hukumance da gwamnati.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

A taron dai, an sanya Abuja a matsayin wurin da taron zaiyi haduwarsa ta karshen badi 2018, saboda ci gaba da yada zumunta da zama lafiya da juna tsakanin al'umma.

Taron ya sami halartar dalibai 135 daga jami'o'in kasar Najeriya. Sannan an tattauna da juna kan yadda kowa ya sami kansa a inda yake a wannan marra.

DUBA WANNAN: Ta Mugabe ta kare a yau Lahadi

Kungiyoyin da suka bada hadin kai taron ya kankama sun hada da IHEU ta duniya, AAI itama ta duniya, da NNHM ta arewacin Najeriya.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Su dai Atishai, wato Atheists da turanci, basu yarda da samuwar ubangiji ba, ba kuma su yarda da duk addinan duniya ba, sai dai sun ce ilimin kimiyya, da zurffin tunani su ne zasu iya yi wa mutane bayanin rayuwa a yadda take, ba tare da imani da ghaybu ba, ko bin chamfi.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

A jawabin Leo Igwe, shugaban kungiyar 'yan Humanist ta kasa, mai kira da a so juna, ya ayyana cewa, son addinai da zain ra'ayi shi ya haddasa Boko Haram da fadan maitatsine a Kano.

Shugaban kungiyar, Callistus Igwuilo, ya yi maraba da manyan baki ya kuma yi bayanin yadda kungiyar ta sami karbuwa da rajista da gwamnati, ba tare da tsangwama ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

A jawabin Mista Bill Flavell, ya bayyana yadda kasashen Turai, suka rungumi Boko, suka manta da addinai, inda a yanzu suke zama lafiya da juna da son juna.

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

A jawabin Miss Roslyn Mould, ta bayyana yadda kungiyarsu ta Atishan kasar Ghana ke taimakawa wajen hana ware wasu mata a arewacin kasar, masu bin addinai na gargajiya da sunan wai mayu ne su.

Mubarak Bala, daga kungiyar 'yan humanist na Arewa, a jawabinsa, ya bayyana yadda ya fahimci addininsa na da wato Islama, da yadda ya gano jihadin su danfodio sak yake da jihadin Boko Haram, don haka ya watsar da imaninsa da gaibu ya kama son jama'a da yada ilimin zamani.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel