Nigerian news All categories All tags
Babu wanda zai iya raba ‘yan kabilar Igbo da Najeriya – Inji Buhari

Babu wanda zai iya raba ‘yan kabilar Igbo da Najeriya – Inji Buhari

- Shugaba Buhari ya ce babu wanda zai iya shiga tsakanin Igbo da kasar Najeriya

- Buhari ya ce Najeriya da Igbo ba za su iya rabuwa da juna ba

- Shugaban kasa ya bukaci ‘yan kabilar Igbo kada su amince da farfagandar ficewa daga Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba ya bukaci dukkan mutanen yankin kudu maso gabashin kasar su yi watsi da abin da ya kira farfaganda a kan fafutukar ficewa daga Najeriya da wasu matasan yankin ke kokarin yi.

Da yake jawabi a filin wasa na garin Abakaliki ranar Talata a lokacin ziyararsa a jihar Ebonyi, Buhari ya jaddada cewa Najeriya da Igbo ba za su iya rabuwa da juna ba.

Ya shaida cewa ‘yan kudu maso gabas mutane ne wanda suke da masaniya da fahimtar akan arakar masana'antu da kuma fasahar kasuwanci kamar yadda 'yan kasuwa na kabilar Igbo suke a duk faɗin Najeriya suna taimakawa wajen bunkasa da ci gaban al'ummar inda suke zaune.

Ba za a iya raba ‘yan kabilar Igbo da Najeriya ba – Inji Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya ce, "Ina rokonku kada ku amince da farfagandar ficewa daga Najeriya" Igbo ita ce Najeriya kuma Najeriya ita ce Igbo, dukansu ba za a iya raba su ba".

KU KARANTA: Nagari Nakowa: Kalli kyawawan hotunan Buhari sanye da kayan kabilar Ibo

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaban ya bayyana cewa ya kasance a Ebonyi a matsayin wata alama ce ta ƙarfin bangaskiya game da hadin kan Najeriya, yana mai cewa kasar ne mafi yawan al'umma a Afirka, tare da fiye da kabilu 300.

Shugaban ya tabbatar wa Ndigbo cewa jin dadi da zaman lafiyar kowane dan Najeriya yana da mahimmanci ga gwamnatinsa, yana mai cewa ba zai bar wata yankin kasar a baya ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel