Nigerian news All categories All tags
Jami’an Yansanda sun halaka wasu masu garkuwa da mutane a Kaduna

Jami’an Yansanda sun halaka wasu masu garkuwa da mutane a Kaduna

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da hallaka wasu da ake zargi sun kashe wani shugaban yan kato da gora dake garin Sabon Gayan, cikin karamar hukumar Chikun.

Mamacin,mai suna Haru Manya ya rasa ransa ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba yayin dayake aiki a gona, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

KU KARANTA: An naɗa shugaba Buhari muhimmin Sarauta a kasar Inyamurai, kalli hotunan naɗin

Kaakakin Yansana, Jimoh Moshood, ya bayyana haka yayi wata ganawa da manema labaru, a garin Gaya, inda yace sun kashe mutanen ne yayin musayar wuta da suka yi da Yansanda.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kaddamar da farautar mutanen ne bayan umarnin da Sufeton Yansanda na kasa ya bayar, na a kamo duk wadanda keda hannu cikin kisan Haru.

A wani labarin kuma, Rundunar Yansanda ta kama wasu masu garkuwa da mutane su 8; Umar Ibrahim, gang leader, Iliya Adamu, Ifeanyi Linus, informant to the gang, Jibril Adamu, Samaila Haruna, Ibrahim Mamman, Ibrahim Idris da Silas Chukwuemeka. Inda yace an ceto mutane 3 daga wajensu.

Jimoh yace sun kwato Motoci guda biyu, kirar Toyota Corolla, kananan bindigu, da da bindiga kirar AK47, da alburusai da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel