Nigerian news All categories All tags
Manyan ayyukan cigaba; Buhari ya ɗau ma Inyamurai alkawari

Manyan ayyukan cigaba; Buhari ya ɗau ma Inyamurai alkawari

Shugaban kasa Muhammadu Buari ya tabbatar ma yan kabilar Ibo cewa gwamnatinsa za tayi musu adalci, kuma zata cika musu alkawurran data daukan musu na kai cigaba yankin.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, yayin ganawa da Sarakunan gargajiyan jihar, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: An naɗa shugaba Buhari muhimmin Sarauta a kasar Inyamurai, kalli hotunan naɗin

“Ziyarar da na kawo a yau, manuniya ce ga burina, na ganin mun kara dankon zumunci a tsakanin al’ummominmu da suka kunshi kabilu daban daban guda 300.

Manyan ayyukan cigaba; Buhari ya ɗau ma Inyamurai alkawari

Buhari

“Yayin ganawa na da shuwagabannin Ibo a fadar gwamnati watan daya gabata, sun nuna damuwarsu ga halin lalacewa da hanyoyinsu suke ciki, da sauran ababen more rayuwa, ina tabbatar muku zamu muku aiki. Kuma mun sanya ayyukan cikin kasafin kudin badi."

A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya kaddamar da wata hanya da gwamnan jihar Umahi ya gina, mai tsayin kilomita 14.5, tare da kaddamar da hanyar sama data shiga har cikin kamaru.

Daga karshe, Buhari ya yaba ma gwamnan jihar saboda irin kokarin dayake yi, sa’annan ya gode ma Sarakunan gargajiya bisa sarauta da suka nada masa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel