Nigerian news All categories All tags
Ku zabi shugaba Buhari domin cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 - Wani Jigo na jam'iyyar PDP ga Inyamurai

Ku zabi shugaba Buhari domin cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 - Wani Jigo na jam'iyyar PDP ga Inyamurai

Wani jigo na jam'iyyar PDP kuma tsohon shugaban majalisar dokoki na jihar Abia, Honorabul Martins Azubuike ya bayyana cewa, gajeruwar hanya da ya kamata inyamurai su bi domin samun shugaban kasa dan kabilar Ibo a shekarar 2023 ita ce, goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a neman takarar sa tta karo na biyu.

Ku zabi shugaba Buhari domin cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 - Wani Jigo na jam'iyyar PDP ga Inyamurai

Ku zabi shugaba Buhari domin cin gajiyar kujerar sa a shekarar 2023 - Wani Jigo na jam'iyyar PDP ga Inyamurai

Tun shekaru aru-aru, 'yan kabilar Ibo ke burin ganin an samu shugaban kasar Najeriya dan kalibar ta su, wanda har ila yau basu yasar da wannan burin na su ba.

KARANTA KUMA: Biyafara: Tayar da kayar baya na Kanu ta na jefa 'yan kabilar Ibo miliyan 11.6 cikin hatsari - Kalu

Azubuike wanda shine shugaban kungiyar magoya bayan shugaban Buhari a jihar Abia, ya bayyana hakan ne yayin da shugaba Buhari ya kai ziyara a yankunan Kudu maso Gabashin kasar da cewa kungiyar kabilar Ibo ta Ndigbo tana goyon bayan shugaba Buhari a yakin sa na neman kujerar shugabancin kasar a karo na biyu.

Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa, hakan zai baiwa 'yan kabilar dama a shekarar 2023 wajen samar da shugaban kasa dan kabilar ta su.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel