Nigerian news All categories All tags
Rayuwa ta tana cikin hatsari - Obiano

Rayuwa ta tana cikin hatsari - Obiano

Gwamnan jihar Anambra Cif willie Obiano, ya bayyana damuwar sa kan yadda aka zare jami'ai da suke bashi kariya, inda ya ce wannan lamari ya jefa rayuwar sa cikin hatsari.

Obiano wanda ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata yayin ganawa da masu ruwa tsaki a taro wanda hukumar zabe ta kasa ta dauki nauyin shirya wa, ya bayyana rashin amince wa da wannan abu da kuma cewar barazana ce ga rayuwar sa sakamakon gabatowar zaben gwamna na jihar.

Cif Willie Obiano

Cif Willie Obiano

Gwamnan ya bukaci da a maido da jam'ai masu bashi kariya domin gujewa barazanar hatsari ba gare shi kadai ba domin kuwa har al'umma. Ya kuma ce duk wanda ke da hannu a cikin wannan lamari sai sun kunya domin kuwa sun shirya wa wannan zabe.

KARANTA KUMA: Biyafara: Tayar da kayar baya na Kanu ta na jefa 'yan kabilar Ibo miliyan 11.6 cikin hatsari - Kalu

A cewar gwamnan, ya kamata su tattauna da sufeto janar na 'yan sanda akan lamarin, sai dai an yi rashin sa'a bai halarci taron ba, wanda hakan ya sanya shi bayyana hakan a bainar jama'a.

Gwamnan ya kuma nuna irin rashin jin dadi yadda ba a ko kula da zuwan shi taron ba, inda shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, wannan taro ne na masu ruwa da tsaki saboda haka babu wani dan takara da za a baiwa fifiko duk da irin mukamin sa.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel